Me ya sa Amurka ta kasa sasanta yaƙi a Gabas ta Tsakiya?
- Marubuci, Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, State Department correspondent
Shekara guda da ta wuce, bayan da Isra'ila ta kaddamar da yaki a Gaza, shugaba Joe Biden ya zama shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara Isra'ila alhalin ana tsaka da yaƙi. Na kalli ziyarar ta sa a Talbijin, yadda hasken abin ɗaukar hoto ke dallare masa idanun a lokacin da yake ganawa da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da majalisar ministocinsa, a lokaccin Biden ya kalli Netanyahu tare da cewa; ''Mu na tare da ku”. Amma ya yi kira ga shugabannin ka da su maimaita kuskuren da Amirka ta yi bayan harin 9 ga watan Satumba.
A satumbar wannan shekarar,a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, shugaba Biden ya jagoranci shugabannin kasasshn duniya da ke kiran Isra'ila da Hezbollah su kai zuciya nesa. Nan ta ke Netanyahu ya maida martani. Isra'ila za ta kurda lungu da sakon yankin domin maida martani da irin makamanta masu cin dogon zango.
Mintina 90 bayan nan, jiragen Isra'ila da Amurka ta ba su ya yi ta luguden wuta kan wani dogon gini a kudancin Beruit. Wannan ne ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah, wannan ya dasa danbar wani gagarumin sha'ani tun bayan kaddamar da yakin da Hamas ta yi ga Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba 2023.
Tuni aka binne batun sasancin diflomasiyya da shugaba Biden ya bijiro da shi a baya, wanda anyi amfani da makaman da kasarsa ta bai wa Isra'ilar gudummawa, tare da maye gurbin shi da martani ta kowacce fuska.
Na shafe kusan shekara guda ina yin nazari kan huldar diflomaisyyar Amirka, na dinga balaguro da abokaina 'yan jarida tare da Sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinkken, da yi ta safa da marwa yankin gabas ta tsakiya, inda kuma nan ne wurin da na yi aiki har tsahon shekara bakwai, kafin barin yankin a watan Disambar bara.
Wani abu da gwamnatin Biden ta ke ta shela tun farkon yakin shi ne batun amfani da matakin diflomasiyya domin tsagaita wuta, da sako wadanda akai garkuwa da su a Gaza.
Sai dai shekara guda kenan da Hamas ta kurda tare da ture duk wani shinge da matakan tsaron da Isra'ila ke alfahari da shi, ta kuma shiga kasar da yin gagarumar barnar da ba a taba yi mata ba, dan haka batun cimma tsagaita wuta ya bi shanun sarki.
Hamas ta kashe sama da Isra'ilawa 1,200, da garkuwa da 250, ciki akwai Amirkawa 7, wasu sun mutu, wasu an kashe su, wasu kuma har yanzu ba a kubutar da su ba.
Sai dai a bangaren Falasdinawa an zubar da jini da salwantar rayukan sama da mutum 42,000, kamar yadda ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta ta bayyana, ana kuma kyautata zaton wasu dubbai na binne karkashin gine-ginen da suka rushe, kusan kashi 80 na gine-gine da gidaje, da makarantu, asibitoci, manyan shaguna, masallatai da majami'u sun zama tamkar kufai.
Halin jin kai ya tabarbare a zirin Gaza, babu ruwan sha mai tsafta, babu makwanci, ga uwa uba matsananciyar yunwa sakamakon toshe shigo da kayan agaji da sojin Isra'ila suka yi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban Falasdinawa sun bata ba a san inda suke ba, an kashe ma'ikatan kungiyoyin agaji da dama, an kai wa motocin agaji hari, amma kullum Isra'ila na ikirarin ta na kauce shafar farar hula.
Yakin ya kara fadada har zuwa yamma da gabar kogin Jordan da yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye, ya kara fadada zuwa kasar Lebanon mai makoftaka wadda mayakan Hezbollah ke marawa Hamas baya, da kuma kasar Iran da ita ce babbar aminiya ga Hezollah da Hamas.
Asara ko Riba
Bibiyar abin da ke faruwa a ma'aikatar cikin gida a Amirka, na yi nazarin tsanaki kan kokarin da gwamnatin Biden ke yi na taimakawa Isra'ila kan jiki kan karfi, da agazawa firai minista Netanyahu tsayawa da kafafunsa. Sai dai manufarta na tsagaita wuta da dakile yakin na fuskantar cikas.
Gwamnatin Biden ta ce sun yi nasarar sauya yadda sojojinta ke gudanar da ayyuka, wani abu da ake ganin matakin Isra'ila na mamayar Rafa da ke kudancin Gaza da aka daidaita, kai babu inda Isra'ila ba ta kurda a Gaza ta lalata ba.
Kafin mamayar Rafah, gwamnatin Biden ta dakatar da tallafin wasu manyan makamai da bama-bama a matakin hana sojin Isra'ila ci gaba da amfani da damar kayan yakin da suke da su wajen kai munanan hare-hare.
Amma ba adauki lokci ba, Amirka ta cire matakin mai kama da takunkumi na takaitaccen lokaci aka ci gaba da tallafawa Isra'ila.
MDD ta ba da rahoton Fari da Yunwa sun samu wurin zama a Gaza, sakmakon hana shigar da tallafin abincin kama daga na MDD har kungiyoyin agaji masu zaman kan su da ma shirin abinci na MDD din, sai dai abin da ake bukata bai kai kashi 10 na wanda ake shiga da shi da kyar da sidin goshi ba.
Yawncin kokarin da ake yi na sasantawa da cimma tsagaita wuta babban manzon Amirka kan harkokin waje Anthony Blinken ne ke jagoranta, ya yi ta zuruftu yankin gabas ta tsakiya kusan sau 10 ko ma fin hakan tun daga watan Oktobar bara, kuma ma'aikatar cikn gida a Amirka ta ce balaguron Mr Blinken ya yi mfani domin an samu shigar da karin agaji ga Falasdinawa, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar Matthew Miller ya bayyana.
Sai dai kamar yadda nai ta bibiyar lamarin, na shaida lokuta mabanbanta da aka gagara cimma tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, duk da tsoma bakin Amirka da wasu kasasshen da ma yankin na gabas ta tsakiya.
An anbato Mr Blinken a lokacin da ya isa kasar Qatar, ya na cewa an yi tattaunawar wayar tarho tsakanin shugabannin Hamas da Sarkin Qatar kuma ana fatan cimma nasara.
Babu wani tabbacin da muke da shi kan ko an yi wannan tattaunawa ko a'a, sai dai gwiwa ta yi sanyi kan balaguron bayan Netanyahu ya ce ya fahimtar da Blinken muhimmancin barin sojin Isra'ila a iyakar Gaza da kasar Masar.
Haka akai ta hawa teburin sasantawa amma ba a cimma wata madaukakiyar tsagaita wutar dindindin ba, sai dai ta wucin gadi da ba ta hana kai hare-hare daga bangarorin biyu musamman sojin Isra'ila.
A balaguron shi na 10 a yankin wanda ya kai a watan jiya, Blinken bai je Isra'ila ba.
Sasancin Diflomasiyya na musamman?
A bangaren masu suka ciki har da tsofafin jami'an gwamnatin Amirka sun rubatawa shugaba Biden budaddiyar wasika, tare da kiran ya kawo karshen tallafin soji na dala biliyan 3.8 na sayan makamai da Isra'ila ta bukata tun farkon yakin.
Sun kuma ce kara mamaya da faddar yakin zuwa Lebanon abin kunya ne da kuma gazawar diflomasiyyar Amirka.
Sai dai aminan Biden sun yi watsi da wannan suka. Sun bada misali da cewa kasasshen Qatar da Masar na aiki da Amirka domin shiga tsakani da Hamas, kuma an cimma nasara a watan Nuwambar bara da aka tsagaita wuta da kuma nasarar sako sama da Isra'ilawa 100 da Hamas ta yi garkuwa da su, da akai musayarsu da Faladinawa 300 da ake tsare da su a wurare daban-daban a Isra'ila.
Amirka ta gargadi Isra'ila kar ta mamaye Lebanon kamar yadda ta yi a Gaza, duk da cewar ana musayar makaman roka tsakanin Sojin da Hezbollah, amma hakan ma ta yi biris.
Sanata Chris Coons na hannun damar Mr Biden ne, wanda ke cikin kwamitin majalisa kan harkokin kasasshen waje, wanda ya yi balaguro zuwa Masar da Saudiyya a shekarar da ta gabata, ya ce a shekarar huldar diflomasiyya ta shiga rudani, ya kara da cewa hakkin na dukkan bangarorin biyu ne da suka ki cike gibin da ke tsakaninsu, amma ba za mu kauda kai kan cewa Hamas ce ta fara takalar fadan nan ba.''
Diflmasiyya ta yi rana?
Ko ma yaya ne ba huldar diflomasiyya ce kadai ta kasance tsakanin shugaba Biden da Netanyahu, domin sun san juna cikin gwamman shekaru. Ko wa ya san karara ya ke nuna dan gani kashenin Isra'ila ne, tun ma lokacin ya na matashin sanata a shekarun 1970.
Ya marawa Yaduwa baya a bayyane ba tare da nuku-nuku ba, babban abn da ake sukar gwamnatinsa shi ne rashin shawo kan zubda jinin Falasdinawa da Isra'ila ke yi a Gaza.
A shekarar shi ta karshe kan karagr mulkin Amirka abin da ba a taba gani ba wato fitowar masu dubban zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a titunan Amirka, amma bai yi ko dar a alakar shi da Netanyahu.
Emiratus Rashid Khalid kwararre kan gabas ta tsakiya a jami'ar Columbia da ke New York, ya ce dama can huldar diflomasiyyar Amirka na tafiya ne da abin d Isra'ila ke muradi. ''Amirka fa diflomasiyyarta akan turbar idan Isra'ila ta bukaci makmai z mu ba ta ta je ta yaki wanda ta so''.
Sai dai yanzu da zabe ke karatowa, a fafatawa tsakanin tsohon shugaban Amirka Donald Trump da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris, ba a tabbatar da wani shiri da suke da shi kan makomar yakin nan da cimma dakatar da bude ba.
Wannan zabe shi ne watakil zai bude wata hanya kan yakin nan, kan ci gaban shi ko akasin hakan, abin jira a gani shi ne ko ta yaya zaben zai sauya yankin gbas ta tsakiya musamman Gaza da Lebanon da Isra'ila ke yaka a halin yanzu?
Lead image credit: Getty
BBC InDepth is the new home on the website and app for the best analysis and expertise from our top journalists. Under a distinctive new brand, we’ll bring you fresh perspectives that challenge assumptions, and deep reporting on the biggest issues to help you make sense of a complex world. And we’ll be showcasing thought-provoking content from across BBC Sounds and iPlayer too. We’re starting small but thinking big, and we want to know what you think - you can send us your feedback by clicking on the button below.
Get in touch
InDepth is the new home for the best analysis from across BBC News. Tell us what you think.
North America correspondent Anthony Zurcher makes sense of the race for the White House in his twice weekly US Election Unspun newsletter. Readers in the UK can sign up here. Those outside the UK can sign up here.